Labarai
Lagos: Adadin mutanen da suka mutu a ruftawar gini ya ƙaru zuwa 36

Rahotonni daga birnin Legas na nuni da cewa, adadin mutanen da suka mutu sakamakon rushewar been nan mai hawa 21 da ake tsaka da ginawa sun kai mutane 36.
Har kawo yanzu masu aikin ceto na ci gaba da aikin ceto mutanen da ke da sauran numfashi a ƙarƙashin ɓaraguzan ginin.
Da tsakar ranar Litinin ɗin makon nan ne ginin wanda ke a unguwar Ikoyi ya rufto tare da danne mutane da dama, inda tun shekaran jiya Talata rabon da a samo wani mutum da ransa.
Tuni dai gwamnatin jihar ta daba umarnin gudanar da bincike kan rusherwar ginin.