Connect with us

Labarai

NDLEA ta Cafke ma’aikatan jirgin ruwa bisa safarar hodar ibilis

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta kama masu aikin lodi da sauke kaya a jiragen ruwa su 12 a tasahar Apapa da ke birnin Lagos bisa zarginsu da hannu a safarar hodar ibilis da kuɗinta ya kai Naira biliyan tara da miliyan dubu ɗari biyar.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar da daraktan yada labarai na hukumar Femi Babafemi, ya fitar a a jiya Asabar a birnin tarayya Abuja.

Wata babbar kotun tarayya da ke birnin Lagos ce dai ta bai wa hukumar damar cafke ma’aikatan biyo bayan wata kara da hukumar ta shigar gaban kotun mai lamba FHC/L/CS/1518/2021,tun a ranar 28 ga watan Oktoba.

Hukumar ta zargi mutanen ne da hannu wajen yin amfani da jirgin ruwa samfurin Vessel MV mallakin ‘yan kasar Singapore wajen shigo da hodar Najeriya wadda ke da nauyin kilo giram Tatatin da biyu da ɗigo tara.

Haka kuma kotun ta amince da bukatar hukumar ta tsare shugaban jirgin ruwan Mista Tanahan Krilerk da kuma wasu ma’aikatan jirgin ƴan kasar wajen su 21.

Tun a ranar 13 ga watan jiya na Oktoba ne hukumar ta cafke jirgin ruwan sakamakon wasu bayanan sirri da ta samu tare da tallafin rundunar sojan ruwan Najeriya da hukumar yaki da fasa kwauri da jami’an tsaro na DSS da kuma jami’an ‘yan sanda.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet