Connect with us

Zamantakewa

Allah ya yiwa Alhaji Sani Dangote rasuwa a Amurka

Allah ya yi wa ƙanin hamshaƙin attajirin nahiyar Afrika kuma mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Dangote Alhaji Sani Dangote ya rasuwa.

Ƴan uwan marigayin ne suka sanar da rasuwar tasa ga manema labarai da safiyar yau Litinin.

A cewarsu Alhaji Sani Dangote ya rasu ne bayan fama da jinya a wani asibiti da ke ƙasar Amurka a daren jiya Lahadi, kuma ana shirye-shiryen dawo da gawarsa Najeriya.

Marigayin ya kasance hamshaƙin ɗan kasuwa mai zuba jari a muhimman sassa na tattalin arziki da suka haɗa da masana’antu da hrkokin noma da na bankuna da kuma harkokin mai.

Ya kuma zauna a hukumar wasu kamfanoni da suka haɗa da Nigerian Textile Mills Plc Nutra Sweet Limited Gum Arabic Limited da Dangote Textile Mills Limited da Alsan Insurance Brokers Dan-Hydro Company Limited Dansa Food Processing Company Limited da kuma Dangote Farms Limited.

Ya kuma Taɓa zama mataimakin shugaban kungiyar masu sana’ar sarrafa ƙaro ta Afirka sannan kuma ya taɓa zama shugaban kungiyar kwallon Polo na Legas sau biyu baya ga kasancewarsa ƙwararren ɗan wasan Polo.

Har ila yau, ya kasance mamba a cibiyar ƙwararrun masu shige da ficen kayayyaki ta jiragen ruwa watau Fellow of Chartered Institute of Shipping of Nigeria kuma Shugaban ƙungiyar masu samar da takin zamani.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet