Connect with us

Featured

Bambancin Ɗan Arewa Da Ɗan Kudu: Jan hankali ga mutanen Arewa

Davido da Rarara dukkaninsu biyun shahararun mawaka ne wadan da suke da masoya da yawa kuma duk su sun nemi masoyansu da su tara masu kudi kuma masoyan na su su ka yi hakan.

Dauda Kahutu Rarara shi ya fara neman masoya da su tara mashi kudi kafin yayi wa shugaba Muhammadu Buhari waka, shi kuma Davido ya nemi na sa masoyan da su tara masa kudi dan ya biya kudin fiton motar da ya saya kuma dukkan su masoyan su sun tara masu miliyoyin naira, sai dai bayan tara masu kudin shi Davido sai ya yanke shawaran baiwa marayu waɗannan kudin, shi kuma Rarara bayan tara masa kudin sai ya raba ma ƴan fim motoci. Duk da dai duk abinda mutum yayi da dukiyar sa ra’ayin sa ne amma ya kamata mu dinga tunanin inda ya fi dacewa da mu yi amfani da arzikin da Allah ya bamu.
Akwai wani abu da ya kamata mu fahimta a nan, shi Davido ya fito ne daga jihar Osun, wanda kuma jiha ce wacce ba ta fukantar matsalar ƴan fashin daji wato Bandits da ƴan gudun hijira kuma babu matsalar talauci da rashin ilimin zamani kamar yadda yake a arewacin ƙasar nan, shi kuma Rarara ya fito ne daga garin Kahutu a karamar hukumar Danja da ke jihar Katsina, kuma yanki ne wanda yake fama da rashin tsaro da ƴan gudun hijira da kuma rashin ilimin zamani da talauci.

Sai dai daga ƙarshe yadda su ka kashe kudin da aka tara masu shi ne ya sanya ni wanan rubutun. Bayan an gama tara wa Rarara kuɗin waka sai ya ɓuge da sayen motoci yana rabawa ƴan fim, ya manta da matsalar rashin tsaro da talauci da ƴan gudun hijira da rashin ilimin zamani da kuma rashin ingantaccen asibitoci da sauran matsalolin yau da kullum da ya addabi jihar sa ta Katsina da ma Arewacin Najeriya baki ɗaya.

Shi kuma Davido da masoya suka gama tara masa kuɗin sai ya ƙara dauko wasu kudin daga aljihunsa ya ƙara da waɗanda masoya su ka tara masa ya ce a rabawa marayu, ya kuma dauko manya Farfesoshi irin su Farfesa Titi Adebayo, da Farfesa Jonathan Nwosu, da Farfesa Asabe Yohana Joel, da Dr Oyolabu da kuma Farfesa Uloma Onuoha domin su tsara yadda kuɗin za su je wajen marayun nan da kuma gudanar da wannan rabo cikin adalci.

Kamar yadda na fada daga farko, ban yi wannan rubutu ba domin ɓatawa wani suna daga cikin waɗannan mawaka ba, a’a sai dai na yi dan in jawo hankalin mu wajen amfani da damar da Allah ya bamu ta hanyar da ta dace. Idan Allah yayi maka alfarma kowacce iri ce ya kamata ka yi amfani da ita ta hanyar da ta dace saboda Allah zai tambaye ka/ki akan wannan ni’imar da yayi maka.

A nan na ke kira a garemu mutanen Arewa da mu san ciwon kanmu, mu sake yadda muke tunani da gudanar da al’amuran mu, idan ba haka ba toh za mu ci gaba da ganin abinda ba mu son gani. Allah ta’ala yasa mu da ce ya kuma bamu ikon yin daidai a cikin dukkan al’amuran mu. Ameen ya Hayyu ya Qayyum.

Ibrahim Tahir ɗan jarida ne kuma mai yin sharhi akan al’amuran yau da kullum ya rubuto daga Abuja

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet