Labarai
Gwamna Masari ya bayyana dalilan da ya sanya mutanen kirki ba shi shiga siyasa a Najeriya

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce rikici da kuma dabanci a siyasa ke hana mutanen kirki shiga harkokin siyasar Najeriya su bayar da gudummuwa.
Jaridar Daily trust ta rawaito cewa Gwamnan Masari ya faɗi haka ne a jihar Gombe, a lokacin da su ka kai ziyarar a madadin kungiyar gwamnonin APC, tare da gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru.
Rahoton Legit ya bayyana cewa Gwamnonin biyu sun kai wannan ziyara ne domin jajantawa gwamnatin Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, bisa rikicin siyasa da ya faru a jihar.
Masari yace “A matsayin shugabannin siyasa, hakki ya rataya a kan mu kare rayuwa da dukiyoyin al’umma. Saboda haka a kowane irin yanayi bai kamata mu saka kanmu cikin rikicin da zai jikkata mutane ko ma ya kashe wasu ba.”
Masari ya yi kira ga yan siyasa baki ɗaya da su zuba ruwan sanyi a zuƙatansu, su nuna wayewa yayin gudanar da harkokin siyasar su. Da yake martani, Gwamna Yahaya, ya nuna matukar jin daɗinsa ga takwarorin nasa bisa nuna damuwarsu kan gwamnatin Gombe da al’ummar jihar.
Ya kuma jaddada cewa babban abinda ya rataya kan kowace irin gwamnati shine ta tsare rayuka da kuma dukiyoyin al’ummarta.
A cikin martaninshi Gwamna Yahaya ya bayyana cewa zaman lafiyar da aka samu a jihar Gombe ya samo asali ne daga kyakkyawan shiri da kuma dabaru.
Yace gwamnatinsa ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a faɗin jihar.