Labarai
Tashin Hankali: Yan Bindiga sun yi garkuwa da DPO a jihar Edo

Wasu rahotanni daga jihar Edo a Najeriya na cewa an yi garkuwa da wani DPO a jihar.
Kafar PRNigeria a ƙasar ta ruwaito cewa an sace ɗan sandan mai suna CSP Ibrahim Aliyu Ishaq wanda shi ne DPO na ofishin yan sanda da ke Fugar, a kan hanyar Auchi zuwa Agenebode a jihar Edo.
Kafin a kai CSP Ishaq jihar Edo a kwanakin baya, ya taɓa aiki a ofishin ƴan sanda da ke Dakata a jihar Kano.
A bana dai an kai hare-hare ga ofisoshin yan sandan Najeriya da dama musamman a kudancin Najeriya inda aka ƙona ofisoshinsu da ƙwace makamansu