Labarai
Jarumar Mata: Ƴar majalisar da ta kai kanta asibiti a keke tana naƙuda

Wata ƴar majalisa a New Zealand ta kai kanta aisbiti saman keke a lokacin da take cikin naƙuda.
Ta haihu bayan sa’a ɗaya da isa asibitin.
“Ban yi tunanin zan yi amfani da keke ba ina naƙuda, amma hakan ta faru,” kamar yaddaJulie Anne Genter ta bayyana a Facebook.
Ba wannan ne karon farko da ta yi haka ba – ta taɓa yi sherkaru uku da suka gabata.
Ta yi suna wajen sha’awar tseren keke.
BBC Hausa