Connect with us

Labarai

Tuɓe Khalifa Muhammadu Sanusi II ya saɓa tsarin mulkin Najeriya – Kotu

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a ranar Talata, ta bayyana cewa korar da aka yi wa Tuɓaɓɓen Sarki Sanusi Lamido Sanusi II daga jihar Kano ya sabawa doka kuma ya saba wa kundin tsarin mulki.

Mai shari’a Anwuli Chikere, a wani hukunci da ya yanke, ya ce dokar majalisar masarautar ta 2019 da gwamnatin jihar ta yi amfani da ita wajen korar Sanusi ta ci karo da kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

A cewar Chikere, kundin tsarin mulkin kasar nan shi ne koli kuma duk wata doka da ta saba da ita to ta zama banza. Alkalin ya bayyana cewa tsohon sarkin yana da ‘yancin zama a ko’ina ciki har da jihar Kano kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Sanusi, wanda aka tsige a ranar 9 ga Maris, 2020, a ranar 12 ga Maris, 2020, ya kai karar Sufeto-Janar na ‘yan sanda (IG) da Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS) a kan abin da ya kira “tsare shi ga barin jihar Kano ba bisa ka’ida ba.”

Haka kuma an shigar da karar mai lamba: FHC/ABJ/CS/357/2020 wadda Babban Lauyan Jihar Kano da Babban Lauyan Tarayya sune a matsayin masu amsa karar na 3 da 4.

Duk da cewa Sanusi bai kalubalanci tsige shi ba, amma tsohon sarkin, ya nemi kotu ta ba shi umarnin wucin gadi na a sarara masa katange shi da akai daga Jihar kano, wanda hakan a cewar sa ya saba da hakkin sa na dan Adam.

Ya kuma kalubalanci wadanda yake kara da cin zarafinsa da take masa hakkinsa. Mai shari’a Chikere, wanda ya cire sunan AGF daga karar, ya kuma hana masu wanda ake kara na 1 da na 2 da na 3 ci gaba da muzguna masa.

Kotun wadda ta ci tarar Naira miliyan 10 ga wadanda ake kara na 1 da na 2 da na 3, ta kuma umarce su da su gabatar da uzuri ga jama’a a cikin jaridu biyu na kasa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet