Labarai
Yadda ɗalibai 20 su ka rasa ransu fiye da 30 su ka ɓata a wani hatsarin Kwale – kwale a Kano

A yammacin jiya Talata aka samu wani rahoto akan cewa mutane da dama ciki har da daliban Islamiyya ne suka mutu sakamakon hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Bagwai da ke jihar Kano.
Rahotannin sun nuna cewa fiye da mutum 30 ne suka bata bayan hatsarin kwale-kwalen da yammacin ranar Talata.
Bayanai sun nuna cewa mutanen sun taso ne daga kauyen Badau zuwa garin Bagwai domin yin maulidi amma kwale-kwalen ya nutse da su.
Tuni rundunar ‘yan sandan jihar ta Kano ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa kwale-kwalen yana dauke da mutum kusan 50.
Kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida wa manema labarai cewa “kwale-kwalen mai dauke da kusan mutum hamsin ya kife a kogin Bagwai.
“Ya zuwa yanzu mun gano gawar mutum ashirin, sai kuma mutum bakwai da aka ciro da ransu sanna ana ci gaba da neman wasu da dama da suka nutse.”
Ganau sun shaida cewa jirgin ya nutse ne a kogin Bagwai sakamakon daukar mutane fiye da kima.
Hatsarin kwale-kwale ba wani sabon abu ba ne a Najeriya lamarin da yake matukar tayar da hankalin mutane saboda rashin daukar matakin dakile shi.