Connect with us

Labarai

Ba zai yiwu mu ci gaba da rayuwa a cikin wannan yanayi na firgici ba – Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasar, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa ba zai yiwu ƴan Najeriya su cigaba da zama cin firgici ba a sakamakon matsalar tsaro.

Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana hakan a cikin sakon ta’aziyyar da ya aike na wasu ƴan cirani fiye da 40 da yan bindiga su ka cinnawa wuta a jihar Sokoto.

“Ina miƙa ta’aziyyata ga iyalai da kuma dukkan mutane da gwamnatin jihar Sokoto, bisa wannan kisan gillar da aka yiwa matafiyan da ba su ji ba su gani ba a kan hanyarsu daga Gidan-Bawa zuwa Sokoto, ranar Laraba 7 ga watan Disamba”

“Na yi takaicin hanyar da waɗannan bayin Allah suka rasa rayuwarsu a hannun ƴan ta’adda. Abun baƙin ciki shi ne yadda kisan kai ya zama ba komai ba a yanzu. Ba zai yiwu ba a matsayinmu na mutane mu ci gaba da rayuwa a cikin wannan yanayi na firgici da tashin hankali da zarar tafiya ta kama mu ba. Ba zai yiwu ba”
Haka kuma Atiku Abubakar ya yi adduar Allah ya yi wa wadanda su ka rasu rahama tare da baiwa iyalansu haƙurin rashi
”

“Ina Addu’ar Ubangiji Ya ji kansu da rahama Ya gafarta musu zububansu Ya kuma baiwa iyalansu haƙurin juriya”

A ranar Talatar da ta gabata ne wasu ƴan bindiga su ka tare wata motar ‘yan ci-rani a ƙauyen Gidan Bawa da ke Sokoto, inda suka kona fasinjoji sama da 40 kurmus.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet