Featured
Buɗaɗɗiyar wasika zuwa ga shugaba Muhammadu Buhari da sauran mahukunta a Najeriya

Amadadin bayin Allah da basu da damar isar da saƙonsu gareku ƴan ƙasa na gari wanda suke kuka ba dare ba rana kan abubuwan da suke faruwa na yawan kashe kashe da hauhawar farashi da jefa al’ummar ƙasa cikin ƙuncin rayuwa.
Muna gujewa gwamnati faɗawa cikin fusatar ɗinbin miliyoyin fusatattun al’umma dake cikin ƙuncin rayuwa wadda suka ga ba ranar fita daga ciki, dan ayi wani Abu kafin lamarin ya kai ga matakin da ba za’a iya shawo kanshi ba aƙanƙanin lokaci, dan hangen mezaije ya dawo.
Muna kira da akawo ƙarshen wannan lamari cikin gaggawa duba ga tsawon lokaci da aka ɗauka ana zubar da jini da asarar rayukan JAMA’A birni da karkara, gidaje da kan tituna, gonaki da makarantu, lamarin da ya zaga ko’ina a arewacin ƙasar nan baki ɗaya ba wani wajen da ake zaune cikin kwanciyar hankali.
Rayuwar takai ga har al’umma sun fahimci rauni akan kulawa da haƙƙoƙin da suka rataya akanku a matsayin shugabanni kuma Wanda aka rantsar akan zaku yi aiki tsakani da Allah sannan zaku kare mana rayukan mu da dukiyoyin mu da samar mana zaman lafiya da kwanciyar hankali ba tare da kun Yi son Rai ko cutar da kowa ba.
Shin Ina wannan rantsuwa da kukayi da alkurani? Shin Ina alƙawarin da kuka ɗauka ?
Shin Baku San abinda ke faruwa bane ? Shin ba zaku iya bane kun kasa ? Kuna da abinda zaku gayawa Wanda kuke wakilta akan wannan YANAYI da ake ciki Wanda ya damu kowa da kowa a ƙasa musanman arewacin ƙasar ?
Idan Baku dubi waɗannan ba a gaba Kuna tunanin zamu sake yarda daku ko mu sake zaɓarku ?
Muna jiranku da gaggawa akan kuyi Zama na musanman Dan kawo ƙarshen wannan lamari hakan ne kadai zai tabbatar Mana cewar Aikin da kuke danmu kukeyinsa, SANNAN kuma a shirye kuke ku sauke nauyin dake kanku ba tare da kun Bari anci gaba da zubar da jini da kashe kashe da ƙone ƙone da cigaba da dorawa Yan kasa wahalhalu ba.
Mutukar Kuna son al’umma suci gaba da binku tare da muku biyayya a zauna lafiya, lallai kuyi abinda ya dace cikin gaggawa da fitowa kuyi magana da ɗaukar dukkan matakan da suka dace, sannan kowanne wakili yayiwa al’ummar sa nagartaccen gansasshen bayani na alƙawarin zakuyi iya iyawarku akan wannan lamari.
A ƙarshe mun faɗa muku sakon da yake damun al’umma kuma muna zuba idanu akan matakin da zaku ɗauka.
Amb Auwal Muhd Danlarabawa
Shugaban Gidauniyar tallafawa mabukata daga tushe (GRASSROOT CARE & AID FOUNDATION).