Connect with us

Labarai

Arewa A Hannun Ƴan Bindiga: Buhari bai damu da rayuwar ƴan Arewacin Najeriya ba – ACF

Ƙungiyar dattawan arewacin Najeriya, watau Arewa Consultative Forum ko ACF ta zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da koyawa gwamnonin arewacin kasar nan nuna halin ko-in-kula dangane da hare haren da ake kaiwa jama’ar yankin ana kashe su a ba tare da nuna wata damuwa ba.

Sanarwar kungiyar wadda ke dauke da sanya hannun Kakakin ta Emmanuel Yawe tace gwamnonin na koyi da halin da shugaban kasa ke nunawa na rashin damuwa da hare haren da ake kai musu da kuma hallaka su.

Emmanuel Yawe ya ce abinda jama’a ke gani daga shugabannin na nuna cewar sun damu da rayuwar su ce kawai tare da ta iyalan su, amma ba na jama’ar da suke yiwa shugabanci ba.

Sanarwar ta ce banda Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum wanda a ko da yaushe ke kan hanyar zuwa wajen jama’ar da yake yiwa shugabanci duk lokacin da aka kai musu hari, shugaban kasa Buhari tare da sauran gwamnonin arewacin kasar basu damu da ziyarar wadanda iftila’i ya afka musu ba, ballanta su jajanta musu.

Yawe ya ce kungiyar ta gabatar da rashin amincewar ta da kuma fushin ta dangane da abinda ta kira amincewa da ci gaba da kashe fararen hula ba tare da kaukautawa ba daga bangaren shugabannin.

Hakazalika ƙungiyar ta ACF ta ce ko a jiya lahadi sai da ƴan bindiga su ka hallaka mutane 38 a ƙaramar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna, kuma basu ga dalilin da ya hana shugaban kasa Buhari da gwamnan jihar Malam Nasir El Rufai ziyarar inda aka kai harin domin jajanta musu ba.

Haka kuma Yawe ya bada misali akan Gwamna Zulum na Jihar Borno wanda a kwanakin nan ya tashi zuwa Askira Uba domin jajantawa mutanen yankin bayan harin da ya hallaka mutane 10.

A ƙarshe ya ce mutanen da suke fuskantar wadannan hare hare a yankin arewacin Najeriya sun yanke yakinin cewar babu wanda ya damu da rayuwar su.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet