Connect with us

Labarai

Rahotanni Na Bayyana Cewa An Yi Garkuwa Da Wasu Ƴan Kasuwa 70 A Kaduna

Rahotanni sun bayyana cewa kimanin sama da ‘yan kasuwa 70 ne ake kyautata zayon an yi garkuwa dasu a ranar Laraba a lokacin da wasu ‘yan bindiga da suka uzzirawa yankin Birnin Gwari suka farmaki ayarin motocin ‘yan kasuwa a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna.

A cewar wata majiya, ayarin motocin sama da 20 wadanda suke tare da rakiyar jami’an tsaron ‘yan sanda wajen jigilar ‘yan kasuwa daga kauyukan karamar hukumar Birnin Gwari zuwa Kaduna da Kano, inda ‘yan bindigar suka afka musu.

Duk da cewa rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ba ta bayar da wata sanarwa a hukumance kan faruwar lamarin ba,sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Muhammed Jalige ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai ya kasa bayar da cikakken bayani kan adadin wadanda ‘yan bindigar suka yi awon gaba dasu, inda ya yi alkawarin zai bayar da cikakkun bayanai game da harin da zarar ya isa ofishinsa.

Wasu majiyoyi sun ce harin ya faru ne da misalin karfe 11:00 na safiyar ranar Laraba, inda aka sace mutanen amma ba a samu asarar rai ba, domin daga baya wasu ‘yan kasuwar sun tsere daga harin, duk da cewa yawancinsu basu yi na sarar tsira ba.

Wani shugaban al’ummar Udawa, Alhaji Muhammadu Umaru, ya shaida wa manema labarai cewa, wasu makwabtan sa hudu na daya daga cikin wadanda ‘yan bindigar suka yi garkuwa dasu.

A cewar Muhammadu, “Harin ya faru ne da misalin karfe 11:00 na safe a tsakanin Udawa da Buruku dake kan babbar hanyar. Inda aka sace hudu daga cikin makwabtana, ‘yan kasuwa ne wadanda suke kan hanyarsu ta zuwa Kaduna da Kano.inda yace Suna cikin ayarin motoci kusan 30 ne karkashin jagorancin rakiyar ’yan sanda.

Kazalika ya kara da cewa “A cikin ayarin motocin, muna da ‘yan kasuwarmu kusan 70 daga garin Udawa kadai, akwai kuma wasu daga garuruwan dake kusa da mu da harin ya rutsa dasu.

Wata majiya ta shaida wa Jaridaralkiblah cewa sama da matafiya 70 ‘yan fashin suka yi garkuwa dasu zuwa cikin daji.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet