Connect with us

Featured

Zan Iya Rantsewa Rabi’u Kwankwaso Ya Fi Duk Gwamnonin Dake Matsa Masa Yin Aiki – Ali Baba Fagge

Babban mashawarci ga gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje akan al’amuran addinai, Ali Baba Agama Lafiya Fagge, yace dukkan gwamnonin  da suka matsawa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, duk ya fisu aiki a Jiharsa.

Suna yi masa baƙin ciki ne kawai saboda sun ga ya fisu farin jini.

Ali Baba Fagge ya bayyana haka ne a daren jiya Laraba cikin wata hira da yayi a Express Rediyo, inda yace shi kansa gwamna Ganduje yana buƙatar gidan Kwankwaso, saboda matsin da yake fuskanta daga tsagin tsohon gwamna Sanata Malam Ibrahim Shekarau, wanda yake janye abokan tafiyarsa na tsohuwar jam’iyyar ANPP irinsu Dan Zago, kuma watakila ma akwai wasu yanzu da muƙamin gwamnati ne yasa basu bi su ba.

A yanzu dai an buɗe e wani sabon babin siyasa a Kano, tun bayan ziyarar ta’aziyya da Ganduje ya kaiwa tsohon mai gidansa Kwankwaso, bisa rasuwar kaninsa Alhaji Inuwa Musa Kwankwaso.

Abin da wasu ke ganin alama ce ta salhu da zai wanzu tsakanin ɓangarorin biyu da aka kwashe tsawon shekaru shida ana taka ledar siyasa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet