Connect with us

Kasuwanci

Kano: Al’ummar Kasuwar Rimi Sun Koka Kan Yadda Aka Rushe Musu Shagunan Su

Wasu ‘Yan Kasuwa a cikin kasuwar Rimi sun Koka kan yanda suka wayi gari da safiyar ranar Talata sun zo Kasuwar suka iske an zuba jami’an tsaro kuma ana yi musu rusau a rumfunan su.

‘Yan Kasuwar dai ta bakin shugaban masu rumfunan da ake rushewa Alhaji Sani Mai turare ya ce sama da shekara 20 karamar hukumar birni ta mallaka musu kuma suna da shedu.

Maiturare ya ce wani mai suna Alhaji Umaru Alasan ya sayi gidan wankan da ke bayan rumfunansu, sai ya gina Shaguna, sai ya nemi su siyar masa rumfunan kasancewar sun nuna masa shedar mallakar rumfunan sama da shekara 20, su kuma su ka je suka tattauna a tsakaninsu suka fada masa farashin rumfunansu 19 Naira 500,000 ko wace daya shi kuma yace sai dai ya siyesu duk akan Naira 500,000.

Maiturare ya kuma ce sakamakon kin amincewa sai ya Garzaya kotu, aka dauki tsahon shekaru 8 ana shari’a a karshe kotu ta bashi tabbacin lokacin da ya sayi gidan wanka hukumar kula tsara burane KNUFDA ta mallaka masa, wanda dama gidan wanka ya siya ne a hannun wani mutum ba a hannun karamar hukuma ba.

Bayan kammala shari’a Alkali ya basu damar daukaka kara idan basu amince ba, sai suka daukaka kara ta bakin lauyansu Barista Abubakar amma bai basu shaidar an daukaka karar ba bai kuma bawa daya tsagin da ake shari’ar da shi ba.

Wannan tasa yau Alhaji Umaru Alasan da rakiyar jami”‘an tsaro da lauyansa suka zo rushe rumfuna.

Shima wani daya daga cikin wadan da aka rushe rumfunan na su Alhaji Iliyasu Kasuwar Rimi ya ce yau da safe suna zuwa suka iske ana rushe musu rumfuna kuma lauyansu ya ce sun daukaka kara.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzasweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişgrandpashabetholiganbetholiganbetgrandpashabetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinograndpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetsahabetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobetjojobet