Labarai
Ƴan bindiga sun sace ƴan China a jihar Neja

Wasu ƴan bindiga sun sace wasu ƴan China huɗu tare da kashe masu tsaron su biyu a jihar Neja da ke yankin tsakiyar Najeriya.
Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Ahmad Matani ne ya tabbatar wa da manema labarai lamarin wanda ya faru a jiya Talata.
Ƴan bindigar sun sace ƴan Chinar ne da ke aiki a Madatsar Ruwa ta Zungeru.