Ilimi
A.A Zaura zai baiwa ɗaliban jihar Kano Tallafin ₦ Miliyan 200

Ɗan takarar gwamnan Kano Abdulkarim Abdussalam Zaura wanda aka fi sani da A.A Zaura zai tallafa wa dalibai ƴan asalin jihar Kano da tallafin kuɗi har naira Miliyan 200
Gidauniyar A.A wato A. A Zaura Foundation ce ta sanar da wadannan makudan kudade har naira miliyan 200 domin tallafawa ɗalibai ƴan asalin jihar Kano dake manywn makarantun kasar nan.
A sanarwar da gidauniyar ta A.A Zaura ta fitar a Kano, Zaura ya ce wannan ɗaya ne daga cikin alƙawurran da yayi a sakon sa na sabuwar shekara da yayi wa mutanen jihar.
” Sanin kowa ne ilimi shi ne ginshikin zaman duniya, a dalilin haka ne zan tallafawa ɗalibai ƴan asalin jihar Kano 10,000 da tallafin naira 20,000 kowannen su.
” Mun samar da fom din da za a cike cikin sauƙi ba tare da an wahala ba. Bayan haka kuma akwai tallafi da Gidauniyar A.A Zaura za ta baiwa mata da kungiyoyi don cigaban al’umma a jihar Kano.
Sai a danna wannan likau ɗin domin samun wannan tallafi: https://aazaura.org.ng/education-support-fund/