Featured
Ta’aziyya: Tunanin Bashir Tofa Kamannin Bashir Tofa

Duk da an tashi da muku-mukun sanyi da iska a ranar Litinin 3 ga watan Janairu 2022 da ta gabata, karfe tara na safe na isa gidan màrigayi Alhaji Bashir Othman Tofa
Ina isowa Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya taso, an dauko gawar Alhaji Bashir Tofa za a ajiye domin sallatarsa. Cikin minti goma an karanta Fatiha, an yi karatun Sura, an yi salatin Annabi SAW, an yi wa BOT addu’a, an yi wa sauran jama’ar Musulmi addu’a da neman gafara, an yi sallama, an yi bankwana, an lalubo gawa, an daga makara, an cicciba an saka a mota. ShIke nan fa.
Wato na ga tashin hankali sosai, a lokacin da naga ana gyara motar daukar gawa da za ta raka wannan bawa zuwa gidansa na karshe. Tsohuwar mota, budaddiya, ga sanyi, ga cinkoso. Duniya ta kare ga Alhaji, kamar yadda ‘yan uwa ke ambatonsa. KAI !!! wannan duniya! a gabana aka sanya wannan kasaitaccen mutum, sarkin kwalliya da ado da tsabta, mai mota da gida, attajiri dan birni, wanda ya kewaye duniya har ya shiga duniyar wata, hadimin marayu, dan kishin kasa, dan arewa na kwarai kuma gwarzon Musulunci cikin mota ta kowa da kowa, kawai sai hawaye ya zubo min.
An yi rashin marubuci da yake magana da zuciyar mai karatu kai tsaye. Masanin dan adam da sararin samaniya. Yau mutuwa ta zo kansa kuma ta tafi da shi. Zuwa goma da rabi na safe har an saka BOT a cikin kabarinsa kusa da mahaifinsa da mahifiyarsa. An tafi an barshi.
Kwana shida ya yi a tsananin rashin lafiya. Yana gida a kwance, dole aka dauke shi zuwa asibitin Mallam Aminu Kano. Amma a tsaitsaye ya yi fama da ciwon suga da uric acid na dan lokaci. Ikon Allah, duk tsawon shekarunsa 75 ba shi da hawan jini. Mutum ne mai tasdiki da imani ga Allah.
Yana cikin mutanen da na kuduri niyyar mu’amilla da su ta kusa, amma Allah bai nufa ba. Saboda na san masani ne da za a sha daga gare shi, wanda Allah ya yi masa tarin baiwa, yana da shekara 19 ya rubuta littafinsa na farko akan aikin hajji wato 1966.Tun ina dan sakandire a shekarar 1986, ina bin sawunsa a rubuce-rubucensa a jaridar Alkalami ta Hausa da The Pen ta Turanci a karkashin Bureau of Islamic Propagation. BIP ita ce ta hada zakakuran marubuta irinsu marigayi Garba Shehu Durbunde da Magaji Galadima da Garba Yusuf Abubakar Garba Isa da Bala Abdullahi Muhammad da Adams Abere da Bashir Othman Tofa. Ita ta farfado da kishin Musulunci da hadin kan malamai bayan rikicin Zangon Kataf na 1987 da karawa JNI da MSS karfi da ingiza NACOMYO da karfafa MSO da FOMWAN. Wannan cibiyar ita ce ta yada karatun Comparative Religion na kaset da bidiyo na Ahmed Deedat.
A lokacin da ina aiki a jaridar AlMizan da The Pointer sau uku ina neman ganawa da BOT a shekarar 1994 abin ya faskara. Sai bayan tsawon shekaru wato a 2004 muka hadu, a shekarar 2017 mun sake haduwa, sai haduwar mu a 2020
Shekara 46 BOT ya yi ba yankewa a siyasa da kasuwanci da harkar addini da gwagwarmayar aikin al’umma wato tun daga 1976. Yana dawowa Najeriya bayan kammala karatunsa na digirin farko akan Business economic management dana biyu aka nada shi kansila mai gafaka, lokacin yana da shekara 29. A 1977 aka zabe shi wakili a kwamitin tsara kundin mulkin kasa wato CDC a Lagos. A wannan shekarar kuma aka fara yunkurin dawo wa mulkin farar hula, inda ya shiga National Movement of Nigeria NPM bangaren matasa. NPM ita ce ta rikide zuwa jam’iyyar siyasa ta NPN ta su Shehu Shagari da Maude Tabacco da Aminu Wali da Ibrahim El Yakub. Bashir Tofa Shi ne sakatare na jiha na farko na NPN a 1979 yana shekara 31. Yana da shekara 32 aka zabe shi sakataren kudi na kasa na NPN a lokacin ya kayar da MKO Abiola dan jihar Ogun duka wannan a jamhuriya ta biyu.
Kafin ya rasu a kwana uku da suka wuce, BOT ya gaya wa mutane da yawa cewa ya daina neman kudi da duk wata harkar kasuwanci har ya koma ga Allah. Zai ci abin da ya tara kuma zai bayar da sauran ga al’umma. Tun da soja suka yi juyin mulki a 1983 ya maida hankalinsa a kasuwanci, abin da ya gada a wajen mahaifinsa. Mahaifinsa Kanuri ne, babban malami da ya zo daga Borno lokacin Sarkin Kano Alu Maisango kuma ya zauna a Dawakin Tofa. Bashir Tofa bai taba yin aikin gwamnati ba. Duk inda ake neman kudi, ya shiga ya buga ya nema. Abu guda da ya tabbatar kafin tafiyarsa lahira, an dade ana cutarsa a kasuwa kuma tun a baya mutane suka fara lalacewa da cin amana.
Da aka kada gangar siyasa a zamanin IBB jamhuriya ta uku a 1990-1992 BOT ya shiga kungiyar Liberal Movement, wacce ta juye zuwa jam’iyyar Liberal Convention daga bisani ta hade da National Republican Convention NRC. A nan ne ya yi takarar shugabancin Najeriya yana da shekara 46. Bashir Tofa abokin Janar Halliru Akilu ne na kusa, shi kuma Akilu abokin Janar Babangida ne. A zaben 1993 wanda BOT ya shiga daga mazabar Gandun Albasa rubdugu yan Santsi mutanen marigayi Rimi suka yi a lokacin yana sharafinsa na siyasa aka zabi MKO Abiola na SDP a Kano, aka kayar da BOT dan sarauta, dan Yolawa, gyauron NPN.
A harkokin siyasar zamanin Abacha, BOT bai shiga sosai ba, amma dan uwansa Abba Othman Tofa, Baba-Sanda ya yi CNC. An dawo kuma jamhuriya ta hudu da muke ciki, BOT da su Mahmudu Waziri da Ummaru Shinkafi da Lema Jibrilu da Sola Saraki suka kafa APP. Daga baya APP ta canza suna zuwa ANPP, a 2007 da 2011 duk sai da ya gwada takarar shugabancin Najeriya a ANPP amma bai samu ba. BOT ba ya canza jam’iyyarsa. Har ya rasu bai taba fita daga ra’ayoyi na ‘yan Liberal ba.
Bashir Tofa ya yi firamare a Yola, sakandire a Gwale da Rumfa College, jami’a kuma a London. Zan shaide shi akan girmama lokaci da cika alkawari da fadar gaskiya akan kowa, irin haka ce ta sanya gwamna Ganduje ya kira shi da Dattijon Wukari.
Yana sha’awar kankareren gini da motar hawa. Mutum ne mai kaifin basira, ya fahimci al’ummar Kano sosai da dabarun yadda za a farfado da tattalin arziki locally da inganta tsaro. Ga shi da hikimomi da dabaru na zance da aiki.
Ya rasu ya bar mata daya da ‘ya’ya shida. Biyar mata, daya namiji. Ruqayya sunan mahaifiyarsa da Usman mahaifinsa sune manyan ‘ya’yansa. Ghali Na Abba dansa ne, Hajiya Rabi mahaifiyar Ghali ita ce ta sha nono ta baiwa Bashir Tofa. Abdurrahman Baffa Yola ma dansa ne.Ya rasu ya bar dubban marayu da littafai 15 da ya rubuta da hannunsa da harshen Hausa da manuscripts birjik
Ya rasu da kokarin tallafawa matasa su zama wani abu. Yana da kishin a barwa matasa dama. Gaskiya matasan baya lokacin samartakar su BOT suna da kishin kasarsu da tarbiyya da manufa, na yanzu duniya da kudi da kwadayi da son alfarma ita ce burinsu. Da yawa a yanzu matasa ba manufa ba ajanda ba abokan tafiya ba dauriya da juriya da tafiya dodar, sannan babu tsari.
Ya rasu yana da tunanin a daina maganar zaben shugabanni ta hanyar ware dan kudu da dan arewa, kawai a koma WAYE wanda ya fi dacewa. Lokacin da shugaban kasa Muhammad Buhari ya mayar da June 12 ranar hutu kuma Democracy Day cewa ya yi ba daidai bane yin hakan.
Ya yi yunkurin kafa sabuwar jam’iyyar siyasa ta arewa da shi da wasu, don a ganinsa PDP ta ‘yan kudu ce, APGA ta Inyamurai ce, APC ma ta ‘yan kudu ce dole a samu Party ‘yar arewa.
Duk da kokarinsa har ya bar duniya bai iya hada kan Mallam Ibrahim Shekarau da Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ba, ga shi kuma tun 2015 ya ke fadi tashi don inganta ci gaban arewa a majalisai birjik irinsu Abuja Round Table da Abuja Chat Room da Kano Elders Forum da Kano Unity Forum da Growth and Development of Northern Nigeria Alhaji Bashir Tofa ya baiwa Sarkin Kano Halifa Muhammad Sanusi II kariya da gudunmawa a lokacin da yana kan mulki kuma yana shugabancin Kano Investment Forum. Duk da kusacinsa da Muhammad Sanusi II an bashi Zannan Kano yaki karba, shi indifenda ne.
Za a dade ba a cike gurbin wannan rashi ba. Bashir Othman Tofa tunaninsa, kamannninsa.
Bello Muhammad Sharada ya rubuto daga Kano