Labarai
Ƴan vigilante sun kama wasu matasa su na feɗe doki domin siyar da naman a Kano

Rundunar Vigilante, reshen unguwar Kundila da ke ƙaramar hukumar Tarauni sun samu nasarar kama wasu matasa da su ka yanka wani doki a Jihar Kano.
Wadannan matasa an kama su ne su uku a lokacin da su ke tsaka da feɗe dokin a cikin wani aji a Makarantar Ƴar Kasuwa Firamare da ke Kundila, a ranar Litinin ɗin.
Ibrahim Muhammad, Mataimakin Shugaban Vigilante na unguwar Kundila, ya tabbatar da faruwar lamarin.
A cewar sa wasu ƴan unguwar ne da su ka ga yaran shi ne su ka kawowa ofishin na su rahoto, inda ya ƙara da cewa jami’an su ba su yi wata-wata ba su ka garzaya wajen.
Da isar jami’an wajen, a cewar Muhammad, sai kuwa su ka iske yaran na feɗe dokin, inda kan ka ce kwabo sun cafke su dukka ukun.
Ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna cewa samarin sun feɗe dokin ne domin sayar da naman ga al’umma a jihar.
Muhammad ya ce tuni dai su ka tattara bayanan farko kuma za su miƙa matasan ga ƴan sanda domin faɗaɗa bincike, inda a hakan za a gano ko ma sato dokin su ka yi ko akasin haka.