Labarai
A ƙarshe gwamnatin tarayya ta janye haramcin da ta saka wa Twitter

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya janye haramcin da ya saka wa Twitter a ƙasar nan.
Mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya tabbatar wa da manema labarai hakan.
Ana sa ran daga 13 ga watan Janairun 2022 matakin na gwamnatin ƙasar zai soma aiki.
Tun a watan Yunin 2021 ne gwamnatin Najeriya ta haramta amfani da Twitter a ƙasar bayan ta yi zargin cewa ana amfani da shafin wajen kokarin tarwatsa kasar ta hanyar yada labaran karya da ke iya haddasa ”tashe-tashen hankula”.