Ilimi
Hukumar TETFund Ta Bukaci Al’umma Da Su Kula Saboda Masu Ayyukan Yaudara

Hukumar kula da manyan makarantun gaba da sakandire (TETFund) ta sanar da jama’a ayyukan damfara da wasu mutane ke yi, suna amfani da sunan asusun a fage daban-daban wajen damfarar mutanen da ba su ji ba su gani ba.
Mukaddashin daraktan hulda da jama’a na TETFund, Mista Abdulmumin Oniyangi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja.
Oniyangi ya ja hankalin masu ruwa da tsaki da sauran al’umma kan ayyukan damfara da ake zargin wasu marasa kirki suke yi wajen damfarar jama’a musamman dalibai.
Mukaddashin daraktan ya ce daya daga cikin hanyoyin damfara da ’yan damfara suka bi shi ne da’awar bayar da tallafi ga daliban Najeriya.
Ya jaddada cewa ana ta yada ikirarin bayar da tallafin ne a shafukan sada zumunta tare da hanyar da ke kai wadanda abin ya shafa zuwa yanar gizo na yaudara.
Oniyangi ya kara da cewa akwai kuma da’awar daukar ma’aikata, jabun wasikun amincewa da shiga tsakani na musamman ga shugabannin cibiyoyin da za su amfana.
Ya bayyana ikirarin tare da gargadin daliban Najeriya da sauran jama’a da kada su fada hannun wadannan marasa kirki.
Ya ce TETFund ba ta cikin wannan zamba kuma duk bayanan karya ne.
Ya shawarci masu ruwa da tsaki da suka hada da daliban manyan makarantun Najeriya da sauran jama’a da su yi hattara da ayyukan damfara da sunan TETFUND.
Ya umarci jama’a da su ziyarci www.tetfund.gov.ng. don ƙarin bayani kan ayyukan TETFUND. (NAN)