Connect with us

Labarai

Babbu Shakka Jam’iyyar PDP Za Ta Samar Da Shugaban Nigeria Na Gaba

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya bukaci ‘yan Najeriya da su cigaba da yin imani da jam’iyyar, yana mai cewa a shirye take ta samar da shugaban kasar na gaba.

Ayu ya ba da wannan tabbacin ne a ranar Lahadi a Fatakwal a wajen taron dare da Gwamna Nyesom Wike na Rivers ya shirya wa gwamnonin PDP.

Ayu, a cikin wata sanarwa da Mista Kelvin Ebiri, mataimaki na musamman ga Wike kan harkokin yada labarai ya raba wa manema labarai, ya cigaba da cewa dole ne a sauya shugabancin jam’iyyar APC a yanzu.

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa ya zargi shugabannin jam’iyyar APC na kasa yin amfani da dimbin arzikin ‘yan Najeriya don samun ingantacciyar rayuwa wanda ya kamata ya karfafa ‘yan uwantaka da inganta zaman lafiya.

“Dole ne mu canza wannan labari kuma hanya daya tilo da za mu canza wannan labari da amfani da ba kawai al’adu ba amma muhalli da wadatar da ke cikinta shine mu marawa PDP baya wacce ta kuduri aniyar samar da sabon shugabanci ga kasar nan,” in ji shi.

Ayu ya kuma ce Najeriya za ta dawo da jam’iyyar PDP a sirdi domin aikin ceto kasar nan da kuma mai da kasar nan mai girma abu ne mai yiwuwa.

Ya bayyana cewa jam’iyyar za ta ba da shugabancin da zai hada kan jama’a a matakin kasa.

“Ba shakka jam’iyyar PDP za ta fitar da shugaban kasa kuma za ta mayar da kasar nan zamanin da muke kan mulki, lokacin da muka cire duk wasu basussukan kasashen waje, lokacin da muke bunkasa kasar nan cikin hanzari,” inji shi.

Tun da farko a nasa jawabin, Gwamna Wike ya ce taron wani kari ne ga taron karba-karba na gwamnonin PDP da aka saba yi.

Ya ce a kodayaushe ana amfani da tarurrukan ne domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi tattalin arziki, siyasa da sauran su da suka shafi zayyana munanan halin al’ummar Najeriya ke ciki.

A nasa bangaren, Shugaban kungiyar Gwamnonin PDP kuma Gwamnan Sakkwato, Alhaji Aminu Tambuwal, ya ce tuni gwamnonin PDP da sauran shugabannin jam’iyyar suka dukufa wajen ganin an sake gina jam’iyyar.

Tambuwal ya ce abun da aka fi mayar da hankali a kai shi ne ceto Najeriya, wanda kuma zai bukaci dukkan ‘yan Najeriya masu kishin kasa su hada karfi da karfe da PDP domin cimma wannan buri.

“Ina kira da kuma rokon duk wani dan Najeriya, hatta wadanda ke cikin APC masu kishin kasa da su hada kai da mu yayin da muke cigaba da yin tattaki domin ceto Najeriya tare,” inji shi.

Gwamnonin da suka halarci wannan taron na dare sun hada da Gwamna Okezie Ikpeazu (Abia), Ahmadu Umaru Fintiri (Adamawa), Udom Emmanuel (Akwa Ibom), Mohammed Bala (Bauchi), Samuel Ortom (Benue), Seyi Makinde (Oyo) da Ifeanyi. Ugwuanyi (Enugu).

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakan gwamnonin Rivers da Zamfara, Dokta Ipalibo Harry-Banigo da Mahdi Aliyu Mohammed Gusau; Sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Sam Anyanwu da sauran manyan baki. NAN

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet