Labarai
Buni Ya Ayyana Ranar Babban Taron Jam’iyyar APC Na Kasa A Watan Fabrairu

Shugaban kwamitin riko na jam’iyyar (APC) Mai Mala Buni ya bayyana ranar 26 ga watan Fabrairu a matsayin ranar gudanar da babban taron jam’iyyar ta APC.
Buni, wanda shi ne gwamnan jihar Yobe, ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wurin taron cigaban mata na kasa na 2022 da aka yi a cibiyar taron kasa da kasa (ICC) da ke Abuja.
Ya ce jam’iyyar tana dogaro da goyon bayan mata don gudanar da babban taron cikin nasara.