Labarai
Sojojin Najeriya sun tarwatsa ‘sansanin ƙungiyar tsagerun IPOB’

Rundunar sojan Najeriya ta ce ta tarwatsa sansanin haramtacciyar ƙungiyar masu neman kafa ƙasar Biafra ta Indigenous People of Biafra (IPOB) da kuma ‘yar uwarta Eastern Security Network (ESN) a Jihar Anambra.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau Talata ta ce haɗin gwiwar dakarunta ne suka kutsa sansanin da ke Ƙaramar Hukumar Ihiala da asubahin Litinin, inda suka kashe wasu daga cikin ‘yan bindigar.
Dakaru sun yi nasarar ƙwace bindigar harba-ruga 10 da waɗanda aka ƙera a gida biyu da kuma sauran ƙananan bindigogi, a cewar sanarwar. Kazalika akwai gatari da tutocin ƙungiyar IPOB da wayoyin salula da ƙananan komfuta.
An kai hare-haren ne da haɗin gwiwar sojojin sama da ‘yan sanda da kuma ‘yan sadan farin kaya na DSS.