Labarai
Rundunar Ƴan Sanda A Kano Ta Cafke Wani Barawo Da Masu Kwace

Rundunar Ƴan Sandan jihar Kano karkashin Kwamishinan Ƴan Sandan CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ta yi nasarar kama wasu Mutane hudu da ake zargin su da aikata laifuka a jihar.
Kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne ya tabbatar wa da KakakiHausa wannan nasara, da cewa an kama su ne a ranar 1 ga watan sabuwar shekara inda jami’an hukumar suka kama wani mutum 1 da zargin satar mota a Garin Mallam, sai wani shima 1 da aka kama da wata mota, daga baya aka kama mutum 2.
Abdullahi Kiyawa ya ce mutane uku sun tare wani mai mashin a hanya da nufin ya taimaka musu motarsu ta sami matsala ya nuna musu wani wuri, suna cikin tafiya ne sai suka shaka masa wani abu kuma daga nan ya rasa hayyacinsa su kuma suka gudu da babir din.
Ya ce bayan kama mutum na farko a mota ne jami’an ofureshin fof ada karkashin jagorancin CSP Hassan Nasir Jega suka kama rogowar 2.
A nasu bangaren mamallakin motar ya ce ya zo wucewane sai motarsa ta lalace, a Kadawa don haka sai ya nemi wane mai farin wani gidan mai a nan sai wani ya fito yace shi ne Mai gadin shi ne ya bashi daga baya kuma yazo ya tarar ya gudu da motar nan take kuma yayi kara a ofishin ‘yan sanda, shi kuma mai babur din ya ce ya taho ne sai wani ya tsayar da shi cewa ya Kashi Multara a gyara musu motarsu za su biyani bayan an gyara ka sai yace na shiga ya famfani bayan mun tafi sai ya bani alewa na sakata a baki na tsotsa sai na jefar da ita, sannan ya bani ruwa nace bana sha, daga nan ban san inda make ba sai ganina nayi a asibiti.
Mutumin da ya saci motar da aka bashi jira ya ce shekarunsa 60 kuma shi dan Zariya ne amma yana zaune ne a Dumaji kasuwan tumatu yake ci, kuma wannan shi ne karo na biyu kuma duk ana kama shi wancen ma sai da yaje gidan yari.
Shi wanda aka kama a cikin motar da aka bayar da kwaya ya ce shekarunsa 48 ya bada aron motar ne ga wadannan mutum 2 sai suka suka je suka aikata laifin, d suke bayanin yanda suka kwace babur din dayan ya ce shekarunsa 35 kuma su ne suka sace babur din yayin da dayan ya ce shekarunsa 47 kuma sun ce duk su 3 suka yi laifin domin da sanin mai motar suka aikata kuma shima ya amsa cewa da saninsa suka aikata.
SP Kiyawa ya ce Kwamishinan Ƴan Sanda ya bada umarnin a gudanar da bincike na kwa-kwaf akai sannan a girfanan da su a gaban kotu tare da shedu da Hujjojin laifin da suka aikata.