Connect with us

Labarai

Kotu a Jigawa ta yankewa wani matashi hukuncin ɗaurin rai – da – rai saboda aikata laifin fyaɗe

Wata babbar kotun jiha da ke zamanta a ƙaramar hukumar Birnin Kudu da ke jihar Jigawa ta zartar da hukuncin ɗaurin rai da rai ga wani matashi ɗan shekara 25 bisa aikata laifin fyaɗe.

Alkalin kotun mai shari’a Musa Ubale ya ce kotun ta samu matashin mai suna Musa Mu’azu dake unguwar Zango a garin Birnin Kudu da laifin yiwa wata yarinya ƴar shekaru 14 fyade wanda hakan ya saba da sashe na 282 ƙaramin sashe na ɗaya na dokar panel code mai lamba 283.

Kotun ta kuma zartar da hukuncin ɗaurin shekaru goma a gidan yari ga wani mai suna Haruna Ali da ke ƙauyen Yarma duk dai a yankin ƙaramar hukumar Birnin Kudu bisa yunƙurin yiwa wata yarinya fyaɗe wanda hakan ya sabawa doka ta biyu ta kare hakkin bil adama ta jihar Jigawa.

Mahukunta dai na yin kira ga mutane da su rika sanya idanu sosai a kan ƴaƴansu, tare da bukatarsu da su mika wa rundunar ƴan sanda rahoton duk wani wanda ya yi wa ‘ya’yan su fyade.

Haka kuma ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta ce duk da cewa fyade laifi ne babba a Najeriya, ana samun ƙaruwar yin sa ne saboda rashin hukunta masu yi a ƙasar nan.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişgrandpashabetholiganbetholiganbetgrandpashabetcasinolevantimajbetsekabetholiganbetholiganbet girişcasibomcasibom girişjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetcasibomcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobetjojobet