Labarai
Waiwaye: Shekaru 10 da kai harin Boko Haram na farko a Kano

Ranar 20 ga watan Janairu shekarar 2012 dai rana ce da mazauna birnin Kano ba za su manta da ita ba, domin kuwa a yammacin ranar ne kungiyar Jama’atu Ahlisuunah Lidda’awati Wal Jihad (Boko Haram) ta kaddamar da hare-hare mafi girma da muni a wasu sassan jihar.
Lamarin dai ya tayar da hankulan mazauna birnin Kano da ba su taba gamuwa da irin sa ba, abinda kuma cikin dan kankanin lokaci ya tsaida al’amura cik a birnin da yafi kowanne hada-hada a arewacin Najeriya, sannan ya bude kofar wasu hare-haren.
Hare-haren da aka kai kimanin ofisoshin jami’an tsaro da dama ciki har da ofishin shiyya ta daya na rundunar ‘yan sandan Najeriya sun janyo mutuwar kimanin mutane 200 a cewar alkaluman hukumomi, sai da mazauna birnin na ganin adadin ya fi haka matuka.
Hare-haren da matakan hukumomi da kuma zaman dar-dar da jama’a ke yi sun durkusar da al’amura a jihar musamman ma na kasuwanci.
An dai dauki sa’o’i da dama ana jefa abubuwan fashewa a wuraren da aka kai hare-haren, gami da musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da kuma maharan a wasu daga cikin wuraren da lamarin ya shafa.
Hare-haren sun sa gwamnati sanya dokar takaita zirga-zirga, sannan jami’an tsaro suka fara kafa wuraren binciken abubuwan hawa, wanda jama’ar birnin basu saba da su ba.
Haka kuma ƴan kasuwa da dama da ke zuwa jihar daga wasu jihohin da ma wasu kasashen domin sayayya sun dakatar da zuwa, sabo da fargaba da kuma zargin cin zarafi daga jami’an tsaro.