Connect with us

Labarai

Rikicin APC A Kano: Badaru da Mai Mala sun fara sulhunta ɓangaren Shekarau da Ganduje

A yau Talata gwamnan jihar Jigawa Mohammed Badaru Abubakar tare da shugaban kwamitin riƙon Jam’iyyar APC, Mai Mala Buni, su ka jagoranci zaman sulhu tsakanin ɓangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da na Sanata Malam Ibrahim Shekarau da ke rigima akan shugabancin jam’iyyar a jihar Kano.

Taron sulhun wanda ya gudana a birnin tarayya Abuja ya samu halartar Sanata Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da tsohon kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogaro da wasu daga cikin yan majalisar wakilai da su ka fito daga jihar Kano.

Da ya ke jawabi bayan kammala zaman sulhun Gwamna Jigawa Badaru Abubakar, ya ce ɓangarorin biyu sun nuna shirin yin sulhu tare da yin aiki tare da kuma mutunta juna wajen gudanar da ayyukan jam’iyyar domin kaiwa ga nasara.

Jam’iyyar APC a Jihar Kano dai ta fada rikicin cikin gida a tsakanin ƴaƴan tun lokacin da aka gudanar da tarurrukan zaɓen shugabanni a matakai daban daban, abinda ya kai ga samun ɓangarori guda biyu da suka hada da na tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau da kuma na Gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje.

Wannan ya kai ga gudanar da tarurrukan jam‘iyyar guda biyu da kuma samun shugabannin bibbiyu a matakai daban daban na jihar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzasweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişgrandpashabetholiganbetholiganbetgrandpashabetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinograndpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetsahabetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobetjojobet