Labarai
Hotuna: Babban Sojin Najeriya Janar Farouk Yahaya ya ziyarci Sarkin Kano

A yau Laraba babban hafsan sojin ƙasan Najeriya, Manjo Janar Farouk Yahaya ya ziyarci mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a fadarsa da ke birnin Kano.
Wannan ne karon farko da Janar Farouk Yahaya ya kawo ziyarar fadar Kano tun lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya naɗa shi a cikin watan Mayun shekarar 2021.