Addini
Musulman jihar Taraba sun koka kan yadda Darius Ishaku ke nuna musu wariya

Majalisar Shura ta addinin Musulunci a jihar Taraba ta yi zargin gwamnan jihar Mista Darius Ishaku da nuna wariya ga al’ummar Musulman jihar a harkar rabon muƙamai.
Shugaban majalisar Shura a jihar Khadi Abdulmumini Abubakar ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Jalingo babban birnin jihar.
A cewar majalisar tun da gwamna Darius Ishaku ya karɓi mulki ya sanya Musulmin jihar a gaba, inda ya riƙa kakkaɓesu ɗaya bayan ɗaya daga kan muƙaman da su ke.
Ya ƙara da cewa matakin da ya ɗauka na baya-bayan nan shi ne na naɗa sababbin manyan sakatarorin ma’aikatun gwamnati guda 13 amma babu ko da Musulmi guda daya a ciki duk da kasancewa akwai daraktoci musulmi da suka kai matsayin da ya kamata a basu wannan mataki.
Haka kuma shugaban majalisar shura ɗin ya ce cikin manyan shugabannin da jami’an gwamnatin Taraba babu Musulmi ko ɗaya.
Al’ummomin Hausawa da Fulani da kuma barebari ‘yan asalin jihar Taraba sun daɗe su na zargin mahukunta a jihar da nuna musu ƙabilanci da wariyar addini.