Labarai
Matasan Najeriya Su Ne Shugabannin Najeriya Na Gobe, Cewar Gbajabiamila

Shugaban Majalisar Wakilai, Honarabul Femi Gbajabiamila, ya ce matasan Najeriya su ne shugabannin kasar na yanzu da kuma nan gaba, don haka ya kamata a ba su goyon bayan da ya dace don samun nasara.
Shugaban majalisar ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a lokacin da yake bayyana bude taron jin ra’ayin jama’a kan kudirin kafa hukumar bunkasa matasa ta kasa da kwamitin matasa na majalisar ya shirya a ranar Alhamis, a zauren majalisar. A cewarsa, dukkanin ayyukan gudanar da mulki da manufofin siyasa dole ne su tabbatar da cewa matasa za su iya yin mafarki manya da kuma cimma babban buri.
“Wannan ya hada da tabbatar da cewa sun sami damar samun ingantaccen ilimi da horo don bunkasa fasahar da ake bukata a cikin tattalin arzikin zamani,” in ji kakakin.
Ya kara da cewa, tuni aka samar da wani kudirin doka da dan majalisar wakilai Simon Karu ya yi don ciyar da shawarwarin manufofi don kafa tsarin daidaita dabarun kasa don inganta zamantakewa, tattalin arziki, da siyasa na matasan kasar.
Da yake karin haske, dan majalisar ya tabbatar da cewa a kan irin wadannan kudirorin, “Shawara ce da za a inganta ta hanyar yin nazari da kuma muhawara mai cike da fahimta yayin da take bin tsarin doka a Majalisar Dokoki ta kasa.
“Matasa su ne al’ummarmu ta yau da gobe. Yakamata a binciko dukkan hanyoyin tabbatar da cewa matasa sun samu jari don kirkire-kirkire da gina masana’antu a kowane fanni na tattalin arziki”.
Gbajabiamila ya yi nuni da cewa, akwai bukatar a yi koyi da ra’ayoyin masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na kasar ta yadda daga irin yadda wadannan ra’ayoyi da dama suka yi yawa, Majalisar Dokokin kasar za ta iya tsara tsarin doka da zai dace da moriyar kasar.
A yayin da yake jaddada cewa dukkan ‘yan majalisar suna da aiki da yawa a gabansu, shugaban majalisar ya kuma ja hankalin takwarorinsa da su yi aikinsu yadda ya kamata ta hanyar tabbatar da cewa gudunmawar da suke bayarwa ta kasance cikin fadakarwa da kuma lura da su, tare da la’akari da dukkan kalubalen da ake fuskanta a kasar nan a yau. kamar yadda damar ta ke da yawa.