Connect with us

Labarai

Majalisar Wakilai Ta Bada Shawarar Kwastam Ta Biya Diyyar Naira Miliyan 360 Kan Kashe-kashen Da Aka Yi

Majalisar wakilai ta umarci hukumar kwastam ta Najeriya da ta biya zunzurutun kudi har naira miliyan 360 ga iyalan mutanen da jami’anta suka kashe a jihohin Oyo da Katsina.

Majalisar ta zartar da wannan kudiri ne a ranar Talata bayan amincewa da rahoton binciken da shugaban kwamitin kwastam Leke Abejide ya gabatar.

An yi la’akari da rahoton kuma an amince da shi a ‘a gaba dayan kwamiti’ karkashin jagorancin Idris Wase, mataimakin kakakin majalisar.

KISAN OYO

Jaridar TheCable ta ruwaito yadda jami’an kwastam suka kashe mutane hudu a garin Iseyin na jihar Oyo a watan Mayun 2021, yayin da suka shiga cikin wadanda ake zargi da yin fasa-kwauri.

A zamanta na ranar Talata, koren majalisar ya umarci hukumar NCS da ta biya naira miliyan 20 kowannen su ga iyalai hudu na wadanda aka kashe a rikicin na Iseyin. Har ila yau, ya bayar da umarnin a biya Naira miliyan 2 a matsayin diyya ga wanda ya samu rauni a harbin bindiga.

Dangane da kashe-kashen da aka yi a Igangan, Igboora, Ayete, Tapa a yankin Ibarapa a jihar, majalisar ta ba da umarnin biyan diyya Naira miliyan 80 ga iyalan mamatan da kuma Naira miliyan 2 ga wadanda aka jikkata.

KISAN KATSINA

Jaridar TheCable ta kuma bayar da rahoton yadda aka kashe mazauna garin a cikin watan Agustan da ya gabata a Katsina bayan da wata motar sintiri ta hukumar NCS ta rasa yadda za ta yi ta yi hatsari a karamar hukumar Jibia ta jihar.

A matsayin diyyar abin da ya faru, ‘yan majalisar sun bukaci a biya kowannen su kudi naira miliyan 20 ga iyalan mutane 1o da suka mutu a wannan bala’in, yayin da a baiwa mutane 13 da suka samu raunuka Naira miliyan 2 kowanne.

Baya ga diyya da aka baiwa wadanda lamarin ya rutsa da su, ‘yan majalisar sun ba da shawarar cewa “a samar da hanyoyin siyan motocin ballistic (harsashi), riguna masu hana harsashi, da huluna cikin gaggawa ga hukumar kwastam ta Najeriya don tinkarar ’yan fasa kwauri da ke kai wa jami’ansu hari a kan iyaka, tashoshi a duk lokacin da masu fasa kwaurin suka bude musu wuta. Hakan zai karfafa hukumar kwastam ta Najeriya kwarin gwiwa wajen dakile fasa kwaurin tare da rage musu wasu dalilai.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet