Addini
Hukumar Hisbah a Kano ta lalata giya ta Miliyoyin Nairori

Hukumar Hisbah mai tabbatar da dokokin Shari’ar Musulunci a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta fasa kwalabar barasa ko giya kusan miliyan huɗu.
Kwamandan Hisba Harun Sani Ibn Sina, shi ne ya jagoranci aikin fasa kwalaben miliyan 3,800,000 a Ƙaramar Hukumar Danbatta ranar Laraba.
Hukumar ta ce ta shafe tsawon lokaci tana tara su bayan ta ƙwace daga hannun ‘yan kasuwar da ke shigar da giya jihar kafin ta fasa su.
A ƙarƙashin dokokin Kano, sayar da giya da sauran kayan maye haramun ne saboda sun saɓa wa kundin Shari’ar Musulunci da jihar ke aiki da shi.