Connect with us

Labarai

Tsohon shugaban ƙungiyar NUJ ya zama hadimin Aisha Buhari

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa Sani Zorro a matsayin Babban Mai Taimaka masa na Musamman a kan Dabarun Hulɗa da Jama’a a ofishin Matar Shugaban Ƙasa.
Zorro tsohon ɗan majalisar wakilai ne daga jihar Jigawa kuma shigaban kungiyar ƴan jaridu ta kasa NUJ.

Babban Mai Taimaka wa Shugaban Ƙasa kan Harkar Yaɗa Labarai, Malam Garba Shehu ne ya tabbatar da naɗin a wata sanarwar da ya fitar a yau Asabar a Abuja.

Garba Shehu ya ce Zorro zai yi amfani da ɗimbin ƙwarewarsa a aikin jarida ta shekara da shekaru, inda ya yi wallafe-wallafe da dama sannan ya riƙa muƙaman ƙungiya a matakai daban-daban.

Ya ƙara da cewa Zorro ya yi Shugabancin Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Ƙasa, NUJ, Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Afirka-maso-Yamma da kuma Taraiyar Ƴan Jaridar Afirka.

Haka kuma Zorro ya rike shugabancin kwamitin kula da harkokin ƴan gudun hijira a Arewa-maso-Gabas lokacin ya na ɗan majalisar wakilai.

Garba Shehu ya kuma sanar da da sauyin wajen aiki na masu muƙaman siyasa uku da ga ofishin Matar Shugaban Ƙasa zuwa ofishin Sakataren Gwamnatin Taraiya kafin da ga bisani a kai su wasu hukumomin da ma’aikatun su ci gaba da aiki a can.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet