Labarai
Siyasar Kano: Muhuyi Magaji ya gana da Aminu Wali

Tsohon shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da hana cin hanci da rashawa na Jihar Kano Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya ziyarci tsohon ministan harkokin waje Ambassada Aminu Bashir Wali a gidansa.
Muhuyi Magaji Rimin Gado wanda ya fice daga jami’yyar APC zuwa jam’iyyar PDP ɓangaren Aminu Bashir Wali, ya kai ziyarar ne a lokacin da jam’iyyar ke fuskantar rikicin cikin gida akan zaɓen shiyyar arewa maso yamma.
Haka kuma Muhuyi Magaji ɗan siyasa ne kuma ɗan gwagwarmaya mai rajin yaƙi da cin hanci da rashawa a jihar Kano.