Connect with us

Labarai

Kotun Ɗaukaka ta ragewa Farouk Lawan shekarun da zai yi a gidan yari

Kotun Ɗaukaka Ƙara a yau Alhamis ta rage shekarun da a ka yanke wa tsohon ɗan majalisar wakilai, Farouk Lawan a gidan yari zuwa shekaru biyar.

A watan Yunin shekarar 2021 ne wata Babbar Kotun Abuja ta kama Lawan da laifuka uku da su ka haɗa da neman rashawa, yarda da karɓar rashawa sannan da ga ƙarshe ya karɓi rashawa ta $500,000 da ga wani ɗan kasuwa, mai suna Femi Otedola.

Daga bisani ne dai kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Angela Otaluka ta yanke wa Lawan hukuncin shekara 7 a kan laifi ɗaya, ya kuma ɗaure shi shekaru 7 a laifi na biyu sai kuma ya ɗaure shi shekara 5 a laifi na uku.

Amma kuma a wani hukunci na bai-ɗaya a yau Alhamis, wani kwamitin mutane uku na kotun daukaka ƙarar, ƙarƙashin jagorancin shugabar kotun, Mai shari’a Monica Dongban-Mensem, ya yi watsi da hukuncin Lawan kan laifi na daya da na biyu.

Kwamitin ya nuna cewa mai ƙara ya gaza fansar da kotu cewa Lawan ya nema da kuma yarda da karɓar rashawa ta dala miliyan 3 da ga Otedola.

Kotun ta tabbatar da cewa mai ƙarar ya iya tabbatar da laifi na uku, wanda ya ke da nasaba da karɓar rashawar $500,000.

Da ga nan ne sai kotun ta wanke Lawan da ga zargin laifi na ɗaya da na biyu, wanda a ka yanke masa shekaru 7 kowanne, amma kuma ta tabbatar da hukuncin laifi na uku, wanda a ka yanke masa shekaru 5.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet