Labarai
Hukumar KAROTA da Civil Defence za su yi aiki tare a Kano

Hukumar da ke kula da zirga-zirgar ababen hawa a jihar wato KAROTA ta bayyana kudurinta na yin aiki tare da jami’an rundunar tsaron kare fararen hula,wato civil defence corps domin tabbatar da ganin al’umma sun bi dokokin hanya da kuma daƙile ayyukan da su ka sabawa da tanadin doka.
Jawabin hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar KAROTA, Nabulusi Abubakar Kofar Na’isa ya fitar.
Nabulusi, ya ce Shugaban Hukumar KAROTA Baffa Babba Ɗan’agundi ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis, lokacin da ya karɓi baƙuncin sabon Kwamandan Tsaron na Civil Defence a ofishinsa.
Baffa Babba ya ce aiki tare da hukumomin tsaro zai ƙarawa jami’an KAROTA karfin gwiwar yin aiki da kuma ganin al’umma sun bi dokokin hanya.
A nasa ɓangaren sabon Kwamandan na CIVIL DEFENCE a jihar Kano, Adamu Idris Zakari ya ce, ya zo hukumar ne domin neman goyon bayanta kan ayyukansa.
Kwamandan ya kuma godewa Baffa Babba kan irin gudunmawar da yake bai wa Rundunarsu, inda ya nemi da ya ruɓanya ƙoƙarinsa domin ciyar da Kano gaba.
A ƙarshe Shugaban Hukumar ta KAROTA ya bayyana cewa zai ci gaba da bai wa Rundunar tsaron ta Civil Defence gudunmuwa, musamman ta ɓangaren gyaran motocin sufurinsu na Rundunar, da sauran buƙatun da suka shafi su domin amfanin al’ummar jihar Kano baki ɗaya.