Connect with us

Labarai

INEC ta saka ranar zaɓukan shekarar 2023 a Najeriya

Hukumar zaɓe a Najeriya INEC ta sanar da jadawalin babban zaɓe na 2023, inda za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa ranar Asabar 25 ga watan Fabarairun 2023.

Shugaban INEC Farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Asabar.

Kazalika, za a gudanar da zaɓen ‘yan majalisun tarayya tare da na shugaban ƙasar.

Zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi zai gudana ranar 11 ga watan Maris na 2023 ɗin.

A cewarsa, an zaɓi ranar ce saboda a tabbatar an yi aiki da sabuwar dokar zaɓe, wadda ta tanadi cewa wajibi ne a bayyana ranar zaɓen aƙalla kwana 260 kafin kaɗa ƙuri’a.

Ya ƙara da cewa hukumar za ta wallafa sauran tanade-tanaden dokar zaɓen “a lokacin da ya dace”.

Sauran ranakun da suka shafi babban zaɓen:

– 28 ga Fabarairu 2022: Wallafa ranakun gudanar da zaɓe.

– 4 ga Afrilu zuwa 3 ga Yunin 2022: Gudanar da zaɓen fitar da gwani na jam’iyyu da kammala sauraron ƙorafe-ƙorafe.

– 10 zuwa 17 ga Yunin 2022: Aika sunayen ‘yan takarar shugaban ƙasa da ‘yan majalisar tarayya ga INEC ta shafinta na intanet.

– 1 zuwa 15 ga Yulin 2022: Aika sunayen ‘yan takarar gwamna da ‘yan majalisar jiha ga INEC ta shafinta na intanet.

– 28 ga Satumban 2022: Fara yawon kamfe na ‘yan takarar shugaban ƙasa da ‘yan majalisun tarayya.

– 12 ga Oktoban 2022: Fara kamfe na ‘yan takarar gwamna da ‘yan majalisar jiha.

– 23 ga Fabarairun 2023: Kammala kamfe na ‘yan takarar shugaban ƙasa da ‘yan majalisar tarayya.

– 9 ga Maris na 2023: Kammala kamfe na ‘yan takarar gwamna da ƴan majalisar jiha.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet