Labarai
Trump ya yi Allah wadai da mamayar da ƙasar Rasha ta yiwa Ukraine

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya yi Allah wadai da mamayar da ƙasar Rasha ta yi wa Ukraine tare da cewa yana yi wa ƴan kasar addu’a.
Mista Trump ya yi kalaman ne a wani taro da aka yi a birnin Florida.
Kalamansa ya sha bamban da wanda ya yi gabannin Rasha ta ɗauki matakin mamayar Ukraine, inda a lokacin da ya yabawa matakin shugaba Vladimir Putin, na tura dakarun wanzar da zaman lafiya Ukraine tare da cewa hakan ya dace.
Ya kara da cewa ya yi amanna Amurka za ta iya daukar irin wannan matakin domin kare tsaron kudancin iyakarta.