Labarai
INEC ta bai wa jam’iyyu wa’adin kwanaki 111 da su mika sunayen ƴan takarar shugaban ƙasa

Hukumar zabe ta ƙasa, INEC, ta umarci jam’iyyun siyasa a ƙasar nan da su mika mata sunayen ‘yan takararsu na shugaban ƙasa daga yanzu zuwa 17 ga watan Yunin 2022.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu, shi ne ya bayyana haka yayin da yake sanar da jadawalin zaben 2023 a taron manema labarai da ya gudanar ranar Asabar a Abuja.
Hakan na nufin dole APC da PDP da ma sauran jam’iyyu da za su fafata a zaben 2023 su aika sunayen masu tsaya musu takarar shugaban kasa nan da kwana 111 masu zuwa.
Ya ce za a “mika fom na tsayawa takarar shugaban kasa da majalisun dokokin tarayya ga INEC ta intanet — daga tara na safen Juma’a 10 ga wata zuwa 17 ga watan Yuni na 2022.”