Connect with us

Labarai

Hukumar KAROTA ta samu nasarar cafke wani matashi bisa zargin satar wayoyin mutane

Jami’an hukumar da ke kula da zirga-zirgar ababen hawa a jihar wato KAROTA sun samu nasarar cafke wani matashi matukin Adaidaita Sahu da zargin satar wayoyin mutane da Adadidaita sahunsa. Jami’an Hukumar KAROTA ne suka cafke matashin mai suna Abdullahi Babakura dan Maiduguri wanda ke sana’ar Adaidaita Sahu a nan kano.

An kama Babakura a wajen tashar mota ta yan kaba a ranar asabar din makon da ya gabata, a lokacin da wani magidanci ya bukaci taimakon jami’an Hukumar wadanda ke a kan titin.

Magidancin ya bayyanawa Hukumar KAROTA cewa, Bayan saukarsa daga Adaidaita Sahun Babakura sai ya fahimci sun dauke masa yawarsa a ciki. Lokacin da aka cafke shi, an same shi da waoyi guda uku kirar androad.

A binciken da Hukumar KAROTA ta gudanar ta gano Babakura na amfani da shigowar baki wanda suke sauka a tashar mota ta Yankaba, idan sun bukaci ya kai su waje sai na dauke su, da zarar sun dauke wayar mutum sai su ce da mutum ya sauka ba nan za su yi ba, kamar yadda suka yi wa wani magidanci mai suna Lawan Abdulkarim lokacin da ya dawo daga tafiya.

Wani shi ma da suka yi masa irin haka makwanni biyu da suka gabata ya bayyana wa Hukumar KAROTA irin dabarun da suke yin amfani da su kafin sace wayar.

Abdullahi Babakura ya bayyanawa Hukumar cewa ba shi kadai yake yin wannan mummunar ta’adar ba, suna yi ne tare da wani abokinsa mai suna Ibrahim Aliyos Kwaya dan unguwar Gama. Tini dai Hukumar ta mika shi ga rundunar Yansanta ta jihar Kano domin fadada bincike. Ko a kwanakin baya ma jami’an hukumar sun cafke wani mashi bisa zargin satar wayoyi da kayan jama’a.

A karshe Shugaban Hukumar Baffa Babba Dan’agundi na kara kira ga jama’a da su dinga kula da kayayyakinsu, musamman idan sun hau Adaidaita Sahu, saboda sabbin dabarun da bata-garin matukan ke amfani da su wajen raba jama’a da kayayyakinsu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet