Featured
Tsakanin Jirgin Air Peace da Tawagar Sarkin Kano

Ana ta yayata cewa kamfanin jirgin sama na Air peace ya ci mutuncin Sarkin Kano, amma idan ka bibiyi labarin zaka sami bayanai sabanin haka. Da farko dai abinda na lura da shi, shi ne yawancin manyan kasarmu su na kokarin bin dokar wasu kasashe sau-ďa-kafa amma da zarar sun iso Najeriya sai su kasance na farko wajen fara karya doka, abinda bai rasa nasaba da yadda muka gina rayuwarmu akan alfarma. Dukkanmu mun ginu a kan assasa alfarma fiye da bin ka’ida. Wannan dabi’a ta samo asali tun zamanin su Sardauna, wadda tushenta ya samo asali daga masarauta.
Shugabanni sun halasta alfarma yadda kowa ya dauke ta abin fahari da koyi. Ko a shagon unguwa, a gidan mai, a layin ATM, asibiti da duk wani sashe na rayuwarmu, kowane talaka na son ya riga dan uwansa samun dama. Wata shekara a Airport din Heathrow dake birnin London muna bin layin shiga jirgi zuwa Abuja sai ga wani gwamna da tawagarsa za su bi wannan jirgi. Da yake a kasar da doka ke aiki ce a kan kowa da kowa ba tare da banbanci tsakanin talaka da shugaba ba, sai ga su gwamna na bin layi a bayanmu. Amma ana zuwa Najeriya sai aka dakatar da mu kan kujerunmu sai da mai girma gwamna ya fita sannan aka bar mu ya-ku-bayi muka sauka. Ya ilahi, idan za ka iya bin dokar wata kasa sau-da-kafa, amma ka kasance kaine na farko da zaka karya dokar taka kasar, menene sunanka?
Abinda ya faru da Sarkin Kano shi ne sun iso Lagos da Asuba daga Banjul za su wuto Kano a jirgin Air Peace, yayinda jirgin ya gama boarding ya na shirin tashi. Sai Isa Sunusi Bayero, wanda aka fi sani da Isa pilot, ya nemi shugaban jiragen ya tsayar da tashin jirgin har sai tawagar Sarki ta fito daga bangaren International Wing na Murtala Mohammed Airport zuwa Domestic wing, wanda zai dauki lokaci. Shugaban kamfanin yayi kokarin jin ta ma’aikatansa da ke Airport wadanda suka shaida masa cewa jirgi ya kammala shirin tashi tsaf don haka maimakon a ajiye fasinja na tsawon kusan awa guda kafin tawagar Sarkin ta iso, sai suka nemi a bar jirgin ya tashi, alabishi Sarkin ya jira zuwa karfe bakwai su hau wani jirgin na Air Peace mai zuwa Abuja tare da alkawarin cewa daga Abuja za su dora tawagar Sarkin a kyauta zuwa birnin Kano. Wannan shawara ba ta yiwa Isa Pilot dadi ba, don haka ya kama yiwa shugaban jiragen dake Airport fada har da yi masa barazanar cewa zai hada shi da mutanen Kano saboda ya wulakanta musu Sarki. Wannan manaja ya bada uzurin cewa hakan ba wulakanci ba ne ga Sarkin, sai ma kokarin kare masa martaba, domin da zarar yan jarida sun sami labarin cewa an dakatar da jirgi cike da mutane na tsawon kimanin awa guda domin a jira Sarki, hakan zai iya ja masa zagi da cece-kuce daga mutanen Najeriya.
Amma kasancewar kasarmu ta zama duk abinda zamu yi, muna kallonsa ko dora shi bisa sikelin banbancin addini, kabila ko yanki, sai ga mutane na ta Allah wadai da wannan jirgi kuma ana ta yayata cewa an wulakanta mana Sarki. Munanan dabi’un alfarma da bangaranci, wallahi har abada ba za su bar mu, mu ga daidai ba a wannan kasa domin tun asali dai alfarma ce ta kassara mu domin ita ta haifar mana da cin hanci da rashawa, shi kuma bangaranci (na yanki, kabila ko addini) shine abinda ya hana mu iya zartar da hukunci a kan laifi, abinda ya sa kowa ke ganin zai iya karya doka kuma ya sha. Duk al’ummar da ba ta san mahimmancin cancanta da ka’ida ba, sannan kuma ba za ta iya yin hukunci na adalci ba, hakika wannan al’umma ba za ta taba ganin daidai cikin al’amuranta ba. A nan arewa kullum mu na tunkaho da musulunci (a baki) amma da zarar an zo aiki sai ka ga cewa wadanda ba musulmi ba sun fi mu kamanta adalci. Shi adalci a musulunci ba shawartamu aka yi da aikata shi ba, wajabta mana shi aka yi, domin Allah ya ce mana cikin suratul Nisa’i
Q4:134 “Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kasance mãsu tsayuwa da ãdalci, mãsu shaida sabõda Allah, kuma kõ dã a kanku ne kõ kuwa, mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko (wanda ake yin shaida a kansa) ya kasance mawadãci kõ matalauci, to, Allah ne Mafi cancanta da al´amarinsu. Sabõda haka, kada ku bĩbiyi son zũciya, har ku karkata. Kuma idan kuka karkatar da magana, kõ kuwa kuka kau da kai, to lalle ne Allah Yã kasance Masani ga abin da kuke aikatãwa.”
Abinda zai ba ka mamaki, wannan aya, saboda irin matukar mahimmancin sakon da ta kunsa, hatta wadanda ba musulmi ba da su ka san abinda ya kamata sun martaba ta, domin idan a yau ka je fannin koyan karatun shari’a (Faculty of Law) da ke jami’ar Harvard, jami’a mafi daraja a duniya zaka tarar wannan aya na daya daga cikin maganganu guda uku mafi mahimmanci da aka zabo daga sassan duniya aka makale su a kofar shiga wannan sashi. Rashin aiki da wannan umarni na Allah shi ya jefa rayuwarmu cikin rudanin da mu ke fuskanta a yanzu kuma matukar ba mu dawo kan wannan koyarwa ba, hakika mu da matsaloli, sai in ce “mutu-ka-raba”.
Ali Abubakar Sadiq ya rubuto daga Kano