Connect with us

Labarai

Har yanzu babu jam’iyyar da ƴan Najeriya ke so sama da APC – El-rufai

Gwamnan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ya yi ikirarin cewa har yanzun al’ummar ƙasar ba su da zaɓin da ya zarce jam’iyyar APC, kuma za ta ci zabe a babban zaɓen shekarar 2023.

Malam Nasiru El-Rufa’i ya ce duk da mutane sun tsammaci abin da ya fi haka, amma idan aka kwatanta ba kamar APC

Ya ce ba ya sha’awar neman wata kujerar siyasa a shekarar 2023, bayan kammala mulkin jihar Kaduna domin yana son hutu

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i, ya ce har yanzun jam’iyyar APC ce zabin yan Najeriya nagari yayin da zaɓen 2023 ke kara matsowa.

Gwamnan ya yi ikirarin cewa jam’iyyarsa ta APC ce za ta samu nasara a zaben shugaban kasa dake tafe.

El-Rufa’i ya yi wannan furucin ne ranar Laraba, yayin zanta wa da kafar watsa labarai ta Channels tv, ya kuma bugi ƙirjin cewa sauran jam’iyyu ba zasu iya kamo inuwar APC ba.
“Ina tunanin yan Najeriya sun yi tsammanin abun da ya fi wanda muka yi, duk da haka idan suka yi nazari a tsanake su sanya sikeli da sauran jam’iyyu, mu ne dai zabin su nagari.”

Tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja ya ƙara da cewa ya na da kwarin guiwar jam’iyyarsa zata sake lashe manyan zaɓuka a 2023.

“Ina da yaƙinin a 2023, jam’iyyar APC zata lashe zaben shugaban ƙasa da kuma mafi yawancin zaɓen gwamnoni a jihohin Najeriya.”

Gwamnan ya bayyana cewa ba ya sha’awar neman wata kujerar siyasa a 2023, a cewarsa bayan kammala mulkin Kaduna yana son hutu.

“Na faɗa na sake faɗa cewa ba zan nemi takara ba, ba na sha’awar kowace siyasa. Idan Rotimi Amaechi na sha’awar neman wata kujera ya na da damar yin haka. Amma ni ba zan nemi komai ba.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet