Labarai
Barack Obama ya kamu da cutar Korona

Tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya ce ya kamu da cutar korona kamar yadda sashen Hausa na BBC ya rawaito
Obama ya sanar da haka ne a Twitter inda ya ce gwaji ya tabbatar da yana da korona.
Tsohon shugaban ya ce yana fama da murar maƙoshi, amma cikin ƙoshin lafiya.
Obama ya kamu da korona ne duk da ya ce an yi masa allurar rigakafin korona.