Labarai
Ko ni ko Tambuwal ko Gwamna Bala duk wanda PDP ta tsayar zamu yi mubaya’a – Saraki

Tsohon shugaban majalisan dattijai, Abubakar Bukola Saraki ya bayyana cewa jam’iyyar PDP a shirye take ta amince da zabin ɗan takaran shigaban ƙasa daya idan hakan ya zama dole a tsakanin su.
Saraki ya bayyana haka a garin Bauchi a lokacin da ya kai ziyara ga gwamnan Bauchi tare da gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.
Dukkan su ukun wato Saraki, Balan Bauchi da Tambuwal duk masu neman takarar shugaban kasa ne a jam’iyyar PDP.
“Abinda ya kawo mu garin Bauchi shi ne don mu gana a tsakaninmu mu ga yadda za a yi a samu daidaito a tsakanin mu duka ƴan takarar domin samun matsaya ɗaya idan da buƙatar hakan”.
“Domin mu samu haɗin kai a tsakanin mu. Kasar nan ita ce a gaban mu ba son rai da burin kowanne ɗayan mu ba”.
“Dukkan mu uku da muka bayyana ra’ayin mu na takarar shugabancin kasar nan, za mu iya. Amma kuma dole mu saka Najeriya a gaba kafin burin mu ya biyo baya.
Sanata Abubakar Bukola Saraki ya ƙara da cewa “Za mu ci gaba da tattaunawa a tsakaninmu domin samun matsaya ɗaya, sannan kuma za mu cigaba da yin haka har sai mun iya cimma matsaya ɗaya a tsakanin mu tukunna domin Jam’iyyar mu da ƙasar mu baki ɗaya.