Labarai
Shugaba Buhari zai kai ziyarar aiki jihar Lagos

A yau Talata ake sa ran shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki a jihar Legas da ke yankin kudu maso yammacin ƙasar nan.
Ana sa ran shugaba Buhari zai ƙaddamar da sabon kamfanin haɗa taki na Dangote baya ga duba wasu muhimman ayyuka da gwamnatin jihar ta Legas ta yi kafin daga baya ya koma birnin Abuja.