Labarai
Engr. Abba Kabiru Yusuf ya fice daga jam’iyyar PDP

Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Kano a zaɓen shekarar 2015 Injiniya Abba Kabiru Yusuf ya fice daga jami’yyar PDP inda ya koma sabuwar jam’iyyar NNPP.
Abba Gida – Gida ya sanar da ficewarsa ne daga jami’yyar PDP a wani taro a ofishinsa da ke mazaɓar Diso da ke yankin ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano.
Engr. Abba Kabir dai na hannun daman tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ne, wanda ya bayyana aniyarsa ta ficewa daga jami’yyar PDP a ƙarshen wannan wata, bayan ƙungiyar sa ta The National Movement (TNM) ta narke a cikin jam’iyyar NNPP.