Addini
Kanawa na nuna kyawawan halaye a lokacin watan Ramadan – Turakin Rano

Ɗaya daga cikin masu zawarcin kujerar gwamnan jihar Kano, a kakar zaɓe mai zuwa ta 2023 a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC mai mulki kuma ɗan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure a zauren majalisar wakilan Najeriya, Kabiru Alhassan Rurum, ya yi kira ga al’umma da su ƙara ƙaimi wajen saudaukar da lokutan ga mahalicci tare da bayar da sadaƙa ga mabuƙata a lokacin watan Azumin Ramadan.
Kabiru Rurum wanda shi ke riƙe da sarautar Turakin Rano, ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai kula da kafafen sada zumuntar sa.
Kazalika tsohon kakakin majlisar jihar Kano, ya ce lokacin azumi lokaci ne da ya kamata Musulmai a Nijeriya da abokanan zamansu suyi amfani da shi wajen yiwa ƙasa addu’a domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da su ta addabi al’umma.
Rurum ya kuma bayyana al’ummar jihar Kano, a matsayin jajirtattu musamman a yayin gudanar da ibada, sadaukarwa da kuma taimakawa mabuƙata musamma a wannan lokaci da aka shiga halin matsin rayuwa da kuma halin rashin tsaro da ya addabi wasu sassan Najeriya.
A ƙarshe ya shawarci al’umma da su dage da addu’o’in neman shugabanci na gari a kowanne mataki a ƙasar nan a yayin da kakar zaɓe ke ƙara tunkaro mu a shekarar 2023.