Labarai
Zan bayyana aniyar tsayawa takarar shugabancin Najeriya a makon gobe – Kwankwaso

Tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya kammala shirin bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 a hukumance, a karkashin jam’iyyar NNPP a makon gobe.
Da ya ke magana a wani taron manema labarai a jiya Juma’a, Kwankwaso ya ce ya yi tuntuɓa da neman shawara kan ƙudurin nasa, inda ya ce ya samu shawarwari masu karfafa gwiwa.
“Na yi ta tuntuɓa ga abokai da ƴan Nijeriya masu ra’ayoyi daban-daban, kuma sakamakon ya kasance mai kyau. Zan sanar da ‘yan Najeriya burina na siyasa a farkon mako mai zuwa,” inji shi.
Tsohon gwamnan ya ce goyon bayan da NNPP ke samu na matuƙar kyau duba da yadda a ke ta samun masu shiga jam’iyar a rajistar zama ɗan jam’iya da aka kammala kwanan nan.
Ya ci gaba da cewa zaɓen 2023 zai kasance ne tsakanin masu son kawo sauyi a al’amuran Najeriya da kuma masu son ci gaba da rike matsayinsu.
Kwankwaso ya kuma yi kira ga gwamnatoci da hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen magance matsalar rashin tsaro, yana mai cewa akwai bukatar gwamnati ta karfafa karfin jami’an tsaro wajen murkushe ‘yan ta’adda.
Ya ce a matsayinsa na tsohon ministan tsaro bai taba tunanin rashin tsaro zai kara ta’azzara ba har ya zuwa yanzu.
Kwankwaso ya ce dole ne shugabancin kasar ya zaburar da kuma horasa da sojoji da kuma samar musu da kayan aikin da ake bukata wadanda dole ne su zarce abin da ‘yan fashi da ‘yan ta’adda ke yi.
“Na yi imanin cewa dole ne gwamnati ta kara yin hakan. Mun damu matuka.
Ya kara da cewa “Na yi imanin tsaro yana daya daga cikin bangarorin da za mu bi tare da iyawa domin ‘yan Najeriya su sake samun ‘yanci don gudanar da harkokinsu na yau da kullum.”