Labarai
Kotu ta umarci shugaban CCT ya gurfana a gaban majalisa

Babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja, ta umarci shugaban kotun da’ar ma’aikata Danladi Umar, ya gurfana a gaban zauren majalisar dattijai domin bahasi kan zargin cin zarafin da aka yiwa wani jami’in tsaro mai zaman kansa a Abuja.
Tun da fari majalisar dattawa ta buƙace shi da ya gurfana gabanta bisa cin zarafin jami’in mai suna Clement Sagwak, wanda ke yin aiki a rukunin shagunan Banex Plaza dake Wuse, 2 a birnin Tarayya Abuja.
Jaridar Solacebase, ta ruwaito cewa an zargi Danladi Umar, da cin zarafin Clement lokacin da ya buƙace shi da ya ajiye motarsa a wajen da ya dace.
Da yake zartar da hukunci game da lamarin, mai shari’a Inyang Ekwo, ya ce, a matsayin Danladi Umar na Jami’in gwamnati da ke gudanar da aikin doka, ya zama wajibi ya gurfana a gaban majalisar domin ba ta bahasi.
Alƙalin, ya kuma yi watsi da roƙon da Danladi Umar ya yi na neman a dakatar da bincikarsa da majalisar ke yunƙurin yi.